Friday, 19 August 2016

Tarihin Misau (part two)

MAMMAN MANGA II (1886-1900)
Bayan mutuwan Sarki Sale said dan sa Mamman manga II ya gaje shi. Ya mulki Misau na shekaru 14. Mamman mutum ne mai basira, ilimi da shugaba mai hikima. Yana da zafi a gudanar da mulki. Baya barin bawa ko kowani mutum ya gudu a wajen yaki. Sarkin ya kuma ci nasaran ciwo yankunan Diri, Yanda Kulus, Gabukka, Takai da Fika. Wannan ya fadada masaratar sosai. A 1990 ya ziyarci surukin sa sarkin Kano Aliyu wanda a hanyar sa ta dawowa Misau ya mutu a Dafo.


AHMADU II (1900 – 1993)
Sarki Ahmadu II kanin Sarki Manga II ne, yayi mulki na shekaru biyu da watanni 9. Lokacin daya tabbatar turawan mulkin mallaka zasu zo su hambarar da mulkin sa, maimakon ya bari su  iso su zubar masa da daraja sai ya yanke shawaran barin Misau  ranar 8th December, 1902. Bayan kwanaki 29 da barin sa sai ya yanke shawaran juyowa gida. Dawowan sa sai ya riske dan uwan sa Alhaji Tafida ya rufe masa kofofin ganuwa. Alhaji tafida yana fatan kalifa zai cire Ahmadu a sarki ya nada shi.
Sarki Ahmadu ya hada sojojin sa yayi wa Misau kawanya na watanni hudu, har April 1903, zuwa lokacin da tsohon Kalifan sokoto, Kalifa Attahiru ya gudu ma turwan burtaniya ya samu Sarki Ahmadu II a wajen ganuwar Misau ya dauke shi suka tafi tare zuwa Burmi.
Bayan anci Attahiru da yaki an kashe shi,  Sarki Ahmadu ya gudu zuwa wajejen Makka. Shi da mutanen sa daga baya suka sauka kusa da kogin Nile a kasar Sudan.

SARKI ALHAJI (1993 – 26)
Bayan guduwan sarki Ahmadu sai turawan Birtaniya suka maida kanin sa Alhaji a matsayin sarki a 1903. An ce gudumawar daya bama baturen burtaniya mai kula da yankin Bauchi Mr. C.L. Temple wajen kama mutanen Sarki Ahmadu a Nafada ya taimaka wajen bashi sarauta.
Turawa sun saka Misau karkashin Katagum, amma daga baya an dawo mata da yancin ta a matsayin masarauta mai zaman kan ta karkashin kasar kano. A 1915 an fadada masarautar tare da kara Dambam da Jalam a karkashin masarautar Misau. A dukkan Lokacin Sarki Alhaji yayi kokari wajen karfafa addnin musulunci a masarautar sa duk da matsin lamba daga turawa. A lokaci guda kuma, an samu bunkasan noma da kasuwanci a zamanin sa, watakila ma saboda ci gaban da sarki ya kawo yasa King George V na England a 26th February 1921 ya bama sarki Alhaji lambar Yabo Medal for  African  Chiefs.  Alhaji Tafida ya mutu ranar juma’a 27th September, 1926.

SARKI AHMADU III (1927 – 1979)
Bayan mutuwan ubansa sai sarki Ahmadu III ya dare karagar mulki daga kujerar sa ta waziri. Sai aka maida Misau Emirate Bauchi province daga Kano province. Sarkin, sarkin gargajiya kuma malamin addini, ya dawo da sunan sarautar sarkin bornu ta gabas wanda sarkin Misau Mamman Manga I ya gada. Ya karbi mulki da kuruciya yana dan shekaru 26 kuma mai ilimi, tsayayye a dukkan matsalolin mulki.
Misau ta ga ci gaba a zamanin sa, ya bada muhimmaci wajen gina makarantun boko tare da islamiyoyi. An nada emirate council lokacin sa, kawo modern agricultural production, postal agency, wutar lantarki, Misau general hospital duk a lokacin sa aka samar dasu. Ya fi kowa dadewa a gadon mulki da shekaru 53. Ya rasu a 1979.

SARKI MUHAMMADU MANGA III (1979 – 2015)
Sarki na 10, ya gaji baban sa. An haife shi 7th September, 1937. Muhammadu Manga kamar kowane sarki ya tashi cikin ilimi. Yayi karatun kura’ani a wajen limamin gari har zuwa 1948 lokacin daya shiga Misau Elementary School. Daga nan ya wuce sannaniyar Bauchi Midle School. Neman ilimin sa ya kaishi har Insititute of Administration, Ahmadu BelloUniversity,  Zaria Karin course kan sha’anin mulki.  Anan ya koyi ilimi wanda zai zaunar dashi cikin shirin zama sarki.
Bayan dawowan sa daga Bauchi Middle school aka bashi Secretary to the emirate council, Misau Native Authority a 1955. A 1958 aka nada shi Hakimin Misau – Yarima. Mukamin da ya rike shekaru 21.
A October 30th,  1979 aka nada shi sarkin Misau na 10 tare da bashi Second Class of Office a 1980. A kasa da shekaru biyu da hawan sa mulki gwamnatin jihar Bauchi taga ya cancanci a maida Emirate din First class status a July 1982.
An samu gagarumin ci gaba a lokacin Manga III. An mayar da Misau Urban Centre bayan State Urban Development Board tayi nazari. Wannan yasa aka sanya Misau akan main National Grid na wutar lantarki, tare da yin hanyoyi irin na birane da tsara gari akan tsarin birni.
Wasu ci gaban sun hada da kafa cibiyar karatun Islama, A.D Rufa’i college for Legal and Islamic Studies, tare da kawo local government cikin masarautar.
A shekaru Alhaji Muhammadu Manga ya karbi lambar yabo da sandunan girmamawa kadan daga ciki; fellowship of administration Management of Nigeria (FIAMN), Lagos; Development in Nigeria Merit Award (DINMA). Sauran sun hada da NEMLA, CDTA, da kuma Honorary Doctorate Degree in Mangament and public Administration from Atlas University, Okija, a Anambra State.
Mafi muhimmaci shine award of the Nigeria National Honors na OON a may 2009.

Sarki Muhammad Manga III ya rasu a August 2015 bayan fama da rashin lapia.

No comments:

Post a Comment