Friday, 19 August 2016

Tarihin Misau (part one

FULATA BORNO

Gwani mukhtar an haife shi a 1738 a wani gari Gurno. Yayi karatun Arabi da addinin Musulunci a wajen wani malami Gwani Lawal a Wuro Bokki. Ya auri yar malamin sa da ake kira Asta. Da mallam Lawal ya mutu sai Gwani Mukhtar ya zama sarkin da kuma limami a wuro bokki.
Imam Gwani Muktar hazikin shugaba ne, mai hakuri, takawa, gaskiya, da kuma adalci. Yayi yake-yake inda ya dinga cin kauyukan kusa da yaki yana musuluntar dasu. 

Tarihin Gwani Mukhtar na farko tarihin Bornu ne bana Misau ba. Lokacin da Imam Gwani Muktar yaji labarin Shehu Usman Danfodio a Saifawa sai ya kai masa Ziyaran Mubayi’a a shekaran 1806, ya kuma juya baya a Sarkin Borno, Mai Dunama, saboda su akwai shirka a cikin musuluncin su. Shehu Usman ya bashi tuta domin ya fita jihadi.daga nan sai ya zabura ya fara yakan garuruwan da suke makwabtaka wadanda bana musulmai ba yana cin su da yaki. Da sarkin Bornu Mai Dunama yaji labari sai ya aika masa da Madakin  sa, Gangarama, zuwa gujba ya yaki Mujaddadi Gwani Muktar, amma Mujaddadi Gwani Muktar ya shi da yaki. Sai karfin mulkin Gwani Mukhtar ya kara tasiri, yaci gaba da yaki yana cin garuruwa yana musuluntar das u. Ya nufi gabashi da yaki yana tafiya ba tare da hamayya ba har ya iso birnin Ngazargamu, Babban birni, fadan masarautar  Bornu,  Yaci garin da yaki bayan an kwafsa yakin kwana biyu kadai. Ya samu nasaran kama Ngazargamu ranan 12th March, 1808.
Mujaddadi Gwani Muktar ya aika babban dan sa Mahammadu Manga ya kai ma mujaddadi shehu usman danfodio labari na aiki mai kyau na jihadi da suke yi shi kuma ya zauna a Ngazargamu na wata bakwai har zuwa lokacin daya karbi order daga shehu usman danfodio ya koma gida. Akan hanyar sa ta komawa gida ne sarkin bornu ya bishi ya kashe shi a watan November 1809. Aka aika dan gwani mukhar Mamman Manga ya tafi da labari ya gaya ma Mujaddi. Shehu ya bama Mamman Tuta a matsayin sarkin Fulata-Borno.
Duk da cewa tushen yan Misau ya samo asali ne daga Bornu, daga wannan lokacin iyi gaba sai harkokin mulkin su ya koma sokoto.
Amma bayan kashe Gwani Muktar sai mutanen Mai Dunama (Bare-bari) suka gudu Birnin Kabella. Bada jimawa ba sai Mamman Manga tare da Mallam Zaki, Sarkin Katagum da Buba Yero, Sarkin Gombe suka kai hari a Birnin Kabella suka ci mutanen Bornu da yaki. Mallam zaki ya ikirarin kasar arewa da Bornu, Buba Yero kasar kudu da bornu sabida taimaka masa a wajen yaki da sukayi. Manga yaki basu kasashen da suka bukata saboda haka suka dawo gida shi kuma ya zauna a bornu.
A daidai wannan lokaci sai Laminu yazo wajen sarkin Bornu Mai Dunama ya masa tayin taimako idan zai bashi kasar da zai zauna a karkashin Bornu. Mai Dunama ya amince sai suka hada karfi suka kori manga zuwa yammacin Gujba. Haka dai suka ci gaba da fada na tsawon shekaru.
Bayan Mamman Manga ya zauna a Gujba na watanni biyar sai ya gina garin kan sa, Damaturu, arewa da Gujba kadan. Anan ne kanin Manga, Aliyu, ya kai kukan Mamman sokoto cewa mutane sun gaji da rashin iya mulki na yayan sa kuma sun fi kaunan sa ya zama sarki akan yayan sa Mamman. Kalifa yayi kokari ya kwantar da hankali sai ya aika wazirin sa, wazirin sokoto Gidado, ya tumbuke Mamman ya nada kanin sa Aliyu sarki. Duk fulanin garin suka bar Damaturu zuwa gudun hijira tare da Mamman Lapia a bornu, suka bar Kanuri kawai tare da Aliyu a Damaturu. Da kalifa yaji haka sai ya order a mayar da Mamman matsayin san a Sarki.
Daga damaturu sai mamman yayi gabar, amma Shehu Laminu ya kore shi zuwa yankin Bauchi. Yakubun Bauchi ya bashi kasa ya zauna a Buri-Buri, daga nan kuma ya dauke shi suka tafi ziyara sokoto.
A sokoto ne aka umurci Yakubu ya yaki Bornu. Bayan Yakubu yayi nasaran ceto Fulani daga tsoron hare-hare na Kanuri bayan sun ci Al-Kanemi da yaki a shekaran 1827, sai yakubu ya hada hannu da Dan Kauwa na Katagum aka kama Misau aka kori mazauna cikin ta a shekaran 1827.
Husuma sai ta kaure tsakanin sarakuna Yakubun Bauchi da Dan Kauwa na Katagum akan mai mallakan Misau, Mamman Manga ya maida jawabi a kalifa Bello, Kalifa ya umurci Yakubu ya maida kasan Misau hannun Mamman Manga, dan Gwani Muktar. Da haka ne Mamman Manga ya zama Sarkin Borno ta Gabas.
A haka manga ya zama sarkin Misau na farko. Amma rundunar Manga ta waste saboda shekara da shekaru na gwabza yaki, sai akayi yarjejeniya zasu bishi Misau ko kuma su dinga aika haraji.
Mamman manga ya mulki Misau na shekaru biyu har zuwa mutuwar sa a 1833 shekarun sa 57 a duniya.


AHMADU (1833 - 1850)
Imam Ahmadu, Da ga Mujaddadi Gwani Muktar, dan uwan Mamman Manga, ya gaji dan uwan sa Mamman. Ya mulki Misau shekaru 17.  A lokacin sa ne aka gina ganuwa, aka kuma gina fadan masarautar Misau. Yayi yake-yake ya ci garuruwa da dama. Ya kai hari ma Tangale fiye das au goma ba tare da nasara ba, a Bornu ma ba nasara (saboda ya rama kasha uban sa Gwani Muktar).  Watakila babban ci gaban da Sarki Ahmadu na farko ya kawo lokacin sa shine fadadan addinin musulunci. ya gina masallatai da islamiyoyi. Ahmadu yayi rashin lapia ya mutu a 1849.

USMAN (1850 - 1861)
Bayan mutuwar Sarki Ahmadu I sai baffan sa (Dan Mamman Manga ne), Usman ya gaje shi. Mayaki mai hidima a addini, Usman, kamar kakannin sa yaci gaba da jihadi. Cikin wadanda yaci da yaki akwai Ma’aniya, Dawa, Tikau da Busongo, sauran sune Iubbi da Kwararrafa a Benue.
A 1855 sarkin gombe kwairanga ya roki Sarki Usman ya taya shi yaki da Tangale. Amma an ci su da yaki. Hakanan a yakin Numan ma sun sha kashi tare da rasa mayaka da yawa.
A cikin gida Usman ya hadu da tawaye. An zarge shi da jawo nasa jiki kawai da Koran wanda ba nasa ba. Yayi mulki shekaru 11 ance kuma sokoto ne suka tumbuke shi a 1861. Masana tarihin Misau sun ce Sale ne ya masa juyin mulki lokacin baya nan yana taya sokoto yaki. Usman ya mutu a gudun hijira a Yelwa, kusa da Bauchi shekara bayan tumbuke shi.

SARKI SALE (1861-86)

Sarki Sale, brother ga sarkiUsman, yayi mulki tsawon shekaru 25. Yayi suna akan yakuna daya ciwo. Yana da mayaka masu masa biyayya. Ance yayi nasarori a yakuna akalla 72. Wasu daga cikin mashahuran yankunan daya kama; maguzawan Wazalenga, Wazza, Kubbi, Waja Talessa a Jihar Gombe. Kare-karen Jalam da Zumbuk da Gala a yankin Warji. Ba mamaki dokin sa – Wauaro har yanzu ana tuna shi. Sale mutum ne mai hazikanci a harkan addini. An kashe shi a yakin Ningawa a Tangali a 1886 shekarun sa 72.

1 comment:

  1. Akwai wayanda suka ruwaita cewa gwani MUKHTAR yanada da Mai suna inrahima Wanda yayi rayuwa tare da sarkin musulmi muhd bello ya auri daya daga cikin kannesa Wanda ya haifi da Mai suna islmail. Sannan Muna son silailar shajara din gwani MUKHTAR inda wasu cikin zuriyarsa suke jinginashi dasharifta wasu kuma suke korewa menene gaskiyar maganar?

    ReplyDelete